Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito, jerin batutuwan Mahdawiyya da ake gabatarwa da taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, an shirya su ne domin yaɗa koyarwa da ilimin da suka shafi Imam Mahdi (AJ), kuma ana gabatar da su ga masu ilimi da masu sha’awar wannan fanni.
Manufofin gwamnatin Imam Mahdi (AS) manufofi ne na gaskiya kuma na asali waɗanda suka samo asali daga zurfin lamirin ɗan Adam. Kowane mutum yana mafarkin samun su. Shirye‑shiryen wannan gwamnati kuma sun ginu ne bisa koyarwar Alƙur’ani da Sunnah na Ma’asumai (AS), kuma a kowane bangare akwai tabbacin aiwatarwa. Saboda haka sakamakon wannan babban juyin juya hali zai kasance mai girma da ban mamaki. A takaice, nasarorin gwamnatin Imam Mahdi (AS) za su biya dukkan bukatun ruhaniya da na zahiri na bil’adama.
Ga wasu daga cikin wadannan nasarori bisa ga ruwayoyi:
1. Adalci Mai Yaduwa
A cikin ruwayoyi da dama, babban sakamakon tashi da juyin juya halin Imam Mahdi (AS) shi ne cika duniya da adalci. A karkashin mulkinsa, adalci zai yadu a dukkan matakan al’umma, har babu wata kungiya ko wata cibiya – babba ko karama – da ba za ta kasance karkashin adalci ba.
Imam Ja’afar al‑Sadiq (AS) ya ce:
«أَمَا وَ اَللَّهِ لَیَدْخُلَنَّ عَلَیْهِمْ عَدْلُهُ جَوْفَ بُیُوتِهِمْ کَمَا یَدْخُلُ اَلْحَرُّ وَ اَلْقُرُّ.» (غیبت نعمانی، ج ۱، ص ۲۹۶)
“Na rantse da Allah, adalcinsa zai shiga cikin gidajen mutane kamar yadda zafi da sanyi ke shiga cikin gida.” (Ghaybat al‑Nu’umani, j.1, sh.296)
2. Ci gaban Hankali, Halayya da Imani
Ruwayoyi sun bayyana cewa a lokacin mulkin Imam Mahdi (AS) hankalin mutane, halayensu da imaninsu za su bunkasa sosai.
Imam Muhammad al‑Baqir (AS) ya ce:
«إِذَا قَامَ قَائِمُنَا وَضَعَ اَللَّهُ یَدَهُ عَلَی رُءُوسِ اَلْعِبَادِ فَجَمَعَ بِهَا عُقُولَهُمْ وَ کَمَلَتْ بِهِ أَحْلاَمُهُمْ.» (کافی، ج ۱، ص ۲۵)
“Lokacin da Qa’im ɗinmu ya tashi, Allah zai sa hannunsa na rahama a kan kawunan bayinsa, ya tattara hankalinsu kuma ya kammala tunaninsu.” (Al‑Kafi, j.1, sh.25)
Saboda haka mafi yawan alheri yana samuwa ne idan hankali ya kammala, domin hankali shi ne “manzon cikin mutum” wanda ke shiryar da shi zuwa ga gaskiya da ibada ga Allah.
3. Hadin Kai da Soyayya
A zamanin mulkin Imam Mahdi (AS), mutane za su rayu cikin hadin kai da juna. Ba za a sami kiyayya ko gaba a zukatan mutane ba.
Imam Ali (AS) ya ce:
«وَلَوْ قَدْ قامَ قائمُنا... لَذَهَبْتِ الشَّحْناءُ، مِنْ قُلُوبِ الْعِبادِ...» (بحارالانوار، ج ۵۲، ص ۳۱۶)
“Lokacin da Qa’im ɗinmu ya tashi… kiyayya za ta gushe daga zukatan bayin Allah.” (Bihar al‑Anwar, j.52, sh.316)
Haka kuma Imam Sadiƙ (AS) ya ce:
«... وَ یَجْمَعَ اَللَّهُ اَلْکَلِمَةَ وَ یُؤَلِّفَ بَیْنَ قُلُوبٍ مُخْتَلِفَةٍ...» (کمال الدین، ج ۲، ص ۶۴۵)
“Allah zai hada kalmar mutane kuma ya sanya soyayya tsakanin zukata masu sabani.” (Kamal al‑Din, j.2, sh.645)
4. Lafiyar Jiki da Ta Zuciya
A gwamnatin Imam Mahdi, cututtuka na jiki da na zuciya za su ragu sosai, kuma karfin jiki da na ruhu zai karu.
Imam Sajjad (AS) ya ce:
«إِذَا قَامَ الْقَائِمُ أَذْهَبَ اللَّهُ عَنْ کُلِّ مُؤْمِنٍ الْعَاهَةَ وَ رَدَّ إِلَیْهِ قُوَّتَهُ.» (غیبت نعمانی، ج ۱، ص ۳۱۷)
“Lokacin da Qa’im ya tashi, Allah zai kawar da kowace cuta daga muminai kuma ya dawo musu da karfinsu.” (Ghaybat al‑Nu’umani, j.1, sh.317)
Ci gaban ilimi da kimiyya a wancan lokaci zai sa a samu magani ga cututtuka da dama.
5. Yawaitar Alheri da Albarka
Ɗaya daga cikin manyan sakamakon mulkinsa shi ne yawaitar albarka. Sama za ta saukar da ruwan sama kuma kasa za ta fitar da amfanin gona.
Imam Sadiƙ (AS) ya ce:
«یَسُوقُ اللَّهُ تَعَالَی بِهِ بَرَکَاتِ السَّمَاوَاتِ وَ الْأَرْضِ فَیُنْزِلُ السَّمَاءُ قَطْرَهَا وَ یُخْرِجُ الْأَرْضُ بَذْرَهَا.» (غیبت شیخ طوسی، ج ۱، ص ۱۸۸)
“Allah zai fitar da albarkar sama da kasa ta wurinsa; sama za ta saukar da ruwan sama, kasa kuma za ta fitar da amfanin gonarta.” (Ghaybat al‑Tusi, j.1, sh.188)
6. Kawar da Talauci
A lokacin Imam Mahdi (AS), albarkatun duniya za su bayyana kuma za a raɓa su da adalci. Saboda haka talauci zai gushe.
Imam Baƙir (AS) ya ce:
«وَ یُعْطِی اَلنَّاسَ عَطَایَا مَرَّتَیْنِ فِی اَلسَّنَةِ وَ یَرْزُقُهُمْ فِی اَلشَّهْرِ رِزْقَیْنِ وَ یُسَوِّی بَیْنَ اَلنَّاسِ حَتَّی لاَ تَرَی مُحْتَاجاً إِلَی اَلزَّکَاةِ.» (بحارالانوار، ج ۵۲، ص ۳۹۰)
“Zai ba mutane kyauta sau biyu a shekara, kuma sau biyu a wata zai ba su arziki, kuma zai daidaita tsakanin mutane har ba za ka ga mai bukatar zakka ba.” (Bihar al‑Anwar, j.52, sh.390)
7. Yaduwar Musulunci da Rushewar Kafurci
Alƙur’ani ya yi alkawari cewa addinin Musulunci zai yi rinjaye a kan sauran addinai:
«هُوَالَّذی اَرْسَلَ رَسُولَهُ بِالْهُدی وَ دِینِ الْحَقِّ لِیظْهِرَهُ عَلَی الدِّینِ کُلِّهِ.» (سوره توبه، آیه ۳۳؛ سوره فتح، آیه ۲۸ و سوره صف، آیه ۹)
“Shi ne wanda ya aiko Manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin ya bayyana shi a kan dukkan addinai.” (Surat al‑Tawbah 33; al‑Fath 28; al‑Saf 9)
A zamanin Imam Mahdi (AS), wannan alkawari zai cika, kuma sakon tauhidi zai bazu a ko’ina.
8. Tsaro Na Gaba ɗaya
A zamanin mulkinsa, tsaro zai wanzu a ko’ina. Ruwayoyi sun bayyana cewa mace za ta iya tafiya daga Iraki zuwa Sham ba tare da tsoro ba.
Imam Ali (AS) ya ce:
«وَ لَوْ قَدْ قَامَ قَائِمُنَا ... لَذَهَبَتِ الشَّحْنَاءُ مِنْ قُلُوبِ الْعِبَادِ وَ اصْطَلَحَتِ السِّبَاعُ وَ الْبَهَائِمُ حَتَّی تَمْشِیَ الْمَرْأَةُ بَیْنَ الْعِرَاقِ إِلَی الشَّامِ لَا تَضَعُ قَدَمَیْهَا إِلَّا عَلَی النَّبَاتِ وَ عَلَی رَأْسِهَا زِینَتُهَا لَا یُهَیِّجُهَا سَبُعٌ وَ لَا تَخَافُهُ.» (خصال، ج ۲، ص ۶۲۶)
“Lokacin da Qa’im ɗinmu ya tashi (ya bayyana), ƙiyayya da gaba za su gushe daga zukatan bayin Allah, kuma namun daji da dabbobi za su sulhunta da juna, har ma mace za ta yi tafiya daga Iraki zuwa Sham ba tare da ta taka ƙafafunta sai a kan tsirrai ba, tana ɗauke da kayan adonta a kanta, babu wani dabbar daji da zai cutar da ita, kuma ba za ta ji tsoronsa ba.” (Al‑Khisal, j.2, sh.626)
9. Yaduwar Ilimi
A zamanin Imam Mahdi (AS), ilimi zai bunkasa fiye da yadda ake tunani.
Imam Sadiƙ (AS) ya ce:
«اَلْعِلْمُ سَبْعَةٌ وَ عِشْرُونَ حَرْفاً فَجَمِیعُ مَا جَاءَتْ بِهِ اَلرُّسُلُ حَرْفَانِ فَلَمْ یَعْرِفِ اَلنَّاسُ حَتَّی اَلْیَوْمِ غَیْرَ اَلْحَرْفَیْنِ فَإِذَا قَامَ قَائِمُنَا أَخْرَجَ اَلْخَمْسَةَ وَ اَلْعِشْرِینَ حَرْفاً فَبَثَّهَا فِی اَلنَّاسِ وَ ضَمَّ إِلَیْهَا اَلْحَرْفَیْنِ حَتَّی یَبُثَّهَا سَبْعَةً وَ عِشْرِینَ حَرْفاً.» (بحارالانوار، ج ۵۲، ص ۳۳۶)
“Ilimi haruffa ashirin da bakwai ne; duk abin da manzanni suka kawo haruffa biyu ne kawai. Lokacin da Qa’im ɗinmu ya tashi, zai fitar da sauran haruffa ashirin da biyar ya yada su tsakanin mutane.” (Bihar al‑Anwar, j.52, sh.336)
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An tsakuro daga littafin “Negine Afarinesh” tare da ɗan gyara.
Ra'ayinka